Bayan harin da sojojin yahudawan sahyuniya suka kai a asibitin Ash-Shifa dake Gaza, majiyoyin labarai sun rawaito cewa kuma sun killace asibitin Al-Ahli.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: A daya daga cikin laifuffukan da suka aikata, sojojin yahudawan sahyuniya sun kashe mutane 30 da suka hada da mata da yara da dama ta hanyar harbin bindiga kai tsaye lokacin da mutanen suke kokarin fita daga asibitin.