23 Yuli 2023 - 08:06
'Yan Shi'ar Afganistan Sun Bukaci Da A Soke Duk Wani Takunkumin Da Aka Sanya Kan Tarukan Muharram

Majalisar malaman Shi'a a kasar Afganistan ta fitar da wata sanarwa inda ta bukaci 'yan Taliban da kada su hana sanya tutocin mazhaba da gudanar da taruka da suka shafi watan Muharram.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Majalisar malaman Shi'a ta Afganistan ta sanar da hakan ne a yayin taron na musamman. An gudanar da wannan taro ne a birnin Kabul tare da halartar dimbin malaman addini, kuma shugabannin 'yan Shi'a na kasar Afganistan sun bukaci da a soke duk wani takunkumin da kungiyar Taliban ta yi kan gudanar da taruka Muharram.