6 Yuli 2023 - 09:37
An Kashe Mutane 13 A Wani Harin Kunar Bakin Wanke A Pakistan

Bayan hare-haren ta'addanci a Pakistan, sojoji da fararen hula da dama ne suka mutu tare da jikkata sakamakon wani harin kunar bakin wake.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Akalla sojoji uku ne suka mutu kana wasu fararen hula 10 suka jikkata a wani harin kunar bakin wake da aka a jiya ranar Laraba a kusa da wani shingen binciken ababan hawa a arewacin Waziristan a lardin Khyber Pakhtunkhwa a arewa maso yammacin Pakistan.

Pakistan dai na fuskantar hare-haren ta'addanci a yankunan Khyber Pakhtunkhwa, Baluchistan da Sindh.

A baya-bayan nan, wani jami'in gwamnatin Pakistan ya sanar da cewa, a kalla jami'in 'yan sanda daya ya mutu, yayin da wasu mutane biyar suka jikkata sakamakon harin da wani dan kunar bakin wake ya kai a kudu maso yammacin Pakistan. Wani jami'in gwamnatin Pakistan "Bashir Ahmed" ya bayyana cewa, wata 'yar kunar bakin wake ta kai hari kan ayarin motocin dakarun sa-kai na jami'an tsaron kan iyakar Pakistan a birnin Torbat na lardin Balochistan.