Shafin yanar gizo na Walla ya bayar da rahoton da ke cewa, kalaman shugaban na Mossad a lokacin zantawarsa da kafafen yada labarai sun haifar da abin kunya a gaban mahukuntan Amurka, bayan da aka shafe kwanaki ana kokarin kwantar da kura a tsakanin bangarorin na Amurka da Isra’ila dangane da yarjejeniyar nukiliya tare da Iran. Shafin ya kara da cewa "Duk da bukatar Lapid, Barnea bai so ya shaidawa manema labarai cewa Amurka ta dage a kan matsayinta a kan batun tattaunawar ba, kuma ya ce wannan matsayi na firaminista ne, kuma bai so ya fadawa manema labarai abin da ke faruwa a tattaunawar da aka yi da Fadar White House ba." Shafin yanar gizon ya nuna cewa "Ofishin Lapid bai yi mamakin bayanin da Barnea ya yi wa manema labarai a ranar Alhamis ba, amma abin mamaki shi ne yin amfani da kalamai masu zafin gaske kan gwamnatin Amurka." Eyal Holata, shugaban kwamitin koli na tsaro a Isra’ila ya mayar da martani daga bangarensa da cewa,
“Lapid da mutanensa ba su ji dadin wannan bangare na jawabin shugaban Mossad ba, wanda kuma tabbas bai yi daidai da sakon da ofishin firaministan Isra’ila ke son a isar ba, kuma bai dace da hakikanin abin da tattaunawar kwamitin tsaron Isra’ila ta kunsa ba." Sannan shafin na Isra’ila ya yi ishara da cewa "kalaman na shugaban kungiyar Mossad sun haifar da abin kunya dangane da Isra’ila a wajen mahukuntan fadar White House, bayan 'yan kwanaki kadan da kawo karshen tayar da jijiyoyin wuya da takun saka tsakanin jami’an gwamnatocin biyu. Ya kara da cewa "bayan an watsa kalaman Barnea, jami'ai a ofishin Firayim Minista sun tuntubi mashawartan shugaban na Mossad, suka nemi a yi musu Karin bayani dangane da kalaman nasa.
" Ya ci gaba da cewa, "Majiyoyi a ofishin Firayim Minista sun ce Lapid ba shi da matsala game da matsayin ƙwararru a ofishin Barnea, kuma ya amince da babban sashi na kwararru na Mossad, amma matsalar ita ce rashin haɗin gwiwa da tuntuba game da wasu saƙonnin da ya isar." A ranar Alhamis din da ta gabata wasu daga cikin kafofin yada labaran Isra'ila sun ba da rahoto game da gargadin da shugaban na "Mossad" David Barnea ya yi, da ke cewa yarjejeniyar nukiliyar da ake shirin yi tare da Iran, yarjejeniya ce mai matukar muni, yana mai jaddada cewa, ya yi Imani Iran ce za ta ci gajiyar wannan yarjejeniya fiye da kowa a tsakanin dukkanin kasashe da suke bangarori ne na yarjejeniyar."
Jaridar "Isra'ila Hayom" a nata bangaren ta bayar da rahoton cewa, Barnea ya ce, a tattaunawar sirri da suka yi a ranar Alhamis, sun kai sakankancewa lalla "Amurka da Iran sun kuduri aniyar cimma yarjejeniya, wadda ake has ashen za a rattaba hannu a kaanta a cikin kwanaki masu zuwa." A cewar jaridar, shugaban na Mossad ya ce "tattaunawar da bangarorin biyu suka yi ta ta'allaka ne kan wasu sauye-sauyen da za a yi, kuma ban ga wani abu da zai hana kulla wannan yarjejeniyar ba." Barnea ya jaddada cewa "Iran za ta samu daruruwan biliyoyin daloli sakamakon dage takunkumin da ta kakaba mata, kuma za ta rage yawan sanadarin uranium da take tacewa a tashoshinta na nukiliya, da sake bude kofa ga jami’an hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA domin su koma su ci gaba da ayyukansu an sanya ido a kan shirinta na nukiliya.
Ya yi nuni da cewa, “Amurkawa sun yi watsi da wasu bukatu na farko, a matsayin wani bangare na yarjejeniyar da aka kulla, ciki har da neman Iran ta ba da amsoshi na tambayoyin da masu bincike na hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa suka yi mata, wanda har yanzu Iran ba ta bayar da gamsassar amsa kan hakan ba, amma kuma Amurka ba ta dauki wani mataki kan hakan ba,” ya kara da cewa Iran za ta fi amfana daga dukkan fa'idodin yarjejeniyar, kuma ba za ta taba da amsa kan tambayoyin da aka yi mata ba, saboda babu wani matsin lamba a kanta dangane da hakan.” Jaridar ta yi nuni da cewa "Shugaban Mossad ya bayyana karara a tattaunawar da ya yi da manema labarai cewa, Isra'ila ba ta da alaka da yarjejeniyar, kuma za ta ci gaba da daukar mataki kan Iran ta kowace hanya domin dakile munanan aniyarta." A cewar Barnea,
"Bayan haka, dole ne mu shirya har zuwa ranar ƙarewar yarjejeniyar, kuma a shirye muke domin mu yi aiki da kanmu don dakatar da Iran daga mallakar makaman nukiliya." A cewar jaridar, Barnea ya kammala da cewa "sakonmu zuwa Iran shi ne cewa za ta iya ci gaba da yin izgili ga kowa yadda ta ga dama, kuma mun san abin da za ta yi ke nan." A nata bangaren, tashar Channel 12 ta Isra’ila nakalto shugaban na Mossad a wasu tarurrukan tsaro cikin gida da aka gudanar, yana mai cewa "yarjejeniya ta yi muni matuka ga Isra'ila, har ma yana kallonta a matsayin babban bala'i ga Isra’ila.
" A safiyar Alhamis din har wala yau, kafofin yada labaran Isra'ila sun ambato tsohon shugaban kwamitin tsaron kasa, Manjo Janar Yaakov Amidror, yana cewa; "Amurkawa sun yaudare mu a baya a yarjejeniyar nukiliyar da ta gabata," yana mai jaddada cewa Amurka ta kasance tana yin aiki ne kawai bisa ga maslaharta”.
Haka nan kuma wasu kafofiin yada labaran na Isra’ila sun yi sharhi tare da bayyana mahangarsu a kan wannan lamari, inda suke bayyana cewa, gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ba ta la'akari da gwamnatin Isra'ila a halin yanzu game dangane da batun hankoron cimma yarjejeniyar nukiliya da Iran. Kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito wata majiyar tsaron gwamnatin yahudawa tana ambaton cewa, Amurka ta yi watsi da dukkanin bukatun Isra’ila dangane da yin watsi da batun cimma yarjejeniya tare da Iran, inda a cewar rahotannin na kafofin yada labaran Isra’ila, majiyar ta bayyana cewa, Amurka ta sanar da Isra’ila cewa, ba zai yiwu a wannan mataki, a dakatar da yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla ba, inda majiyar tsaron gwamnatin yahudawan Isra’ila ta ce, Iran ta samu garabasa a sama.
Har ila yau, ita ma tashar "Channel 13" ta Isra'ila ta nakalto wata majiya mai karfi ta siyasa tana cewa "al'amarin bai yi kyau ba," majiyar ta kara da cewa "abu mafi rauni shi ne yadda aka nuna halin ko in kulak an rahotannin masu bincike na hukumar makashin nukiliya ta duniya, da ke nuna shakku kan wasu aikace-aikacen Iran a wasu tashoshinta na nukiliya, wanda ya kamata a ce bisa ga wanann bincike, yarjejeniyar ta mutu murus. Haka nan kuma wasu rahotannin kafofin yada labaran Isra'ila, sun nakalto majiyoyin siyasa na gwamnatin yahudawan na cewa, "Iran na gab da kulla yarjejeniyar nukiliya tare da manyan kasashen duniya," suna bayyana cewa "Isra'ila na kallon yarjejeniyar da ake yi a halin yanzu a matsayin wata mummunar yarjejeniya ta tarihi. Amir Bukhbut mai sharhi kan harkokin soji na shafin yanar gizo na Wallah na Isra'ila ya ce: "Isra'ila ba za ta yi shiru ba kan abubuwan da ke faruwa a tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka kan batun nukiliyar.
" Shafin ya ce, shugaban na Mossad "shi ne babban mai matsa lamba kan batun Iran a cikin gwamnatin Isra'ila," yana mai cewa, a cikin shekarar da ta gabata, das u Lapid suka karbi gwamnati, daga lokacin lamurra suka canja, inda Isra’ila take nuna rauni da gazawa wajen tunkarar batun yarjejeniyar nukiliya kan shirin Iran, wanda kuma wannan raunin ne ya kai ga halin da ake ciki yanzu. Barnea ya yi iƙirarin cewa dukkanin hukumomin tsaro na soja suna goyon bayan matsayinsa na adawa da yarjejeniyar nukiliya," ya kara da cewa, hatta babban hafsan hafsoshin sojin Aviv Kohavi, yana goyon bayansa wajen ganin an kawo cikas tare da hana aiwatar da wanann yarjejeniya tare da Iran.
Shafin ya bayyana cewa "akwai karo da juna a cikin matakai da matsaya daban-daban da jami’ai na soji da leken asiri da sauran bangarorin tsaro na Isra’ila da ‘yan siyasa suke dauka, kan batun tunkarar batun na Iran. To koma dai yaya lamarin yake, abin da yake faruwa ya kara tabbatar da cewa, batun cimma matsaya domin farfado da yarjejeniya kan shirin Iran na kan hanyar tabbata, kuma wani abu mafi daukar hankali shi ne, yadda lamarin yake gudana a kan sharuddan da Iran kasar ta gindayawa Amurka da kasashen turai, wanda kuma shakka babu hakan lamari ne dab a zai taba yi wa Isra’ila dadi ba.