23 Agusta 2022 - 16:52
Turkiyya, Ta Karbi Bakuncin Abass, Bayan Kulla Alakarta Da Isra’ila

Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abass, ya fara wata ziyarar aiki a kasar Turkiyya, inda zai gana da takwaransa Recep Tayyib Erdogan.

Ziyarar ta kwanaki uku bisa gayyatar shugaba Erdogan a cewar kamfanin dilancin labaren Anadolu na Turkiyya wata dam ace ga bangarorin biyu na su tattauna kan batutuwan da suka shafi karfafa alaka da kuma hulda.

Sannan zasu tattauna batutuwan da suka kasa da kasa da yankin da kuma batun rikicin falasdinu da Isra’ila.

Ziyarar ta shugaban falasdinawan a Turkiyya na zuwa ne mako guda bayan da Turkiyya da Isra’ila suka sanar da dawo da gabadayen alaka a tsakanin tare da musayar jakadu.

Turkiyya dai ta sanar cewa dawo da alakarta da Isra’ila baya nufin ta juya wa gwagwamayar falasdinawa baya, face ma wata dama ta tattauna batutuwan da sukafi rikicin Isra’ila da falasdinu kai tsaye da mahukuntan Tel Aviv, a cewar ministna harkokin wajen Turkiyya.

342/