18 Mayu 2022 - 19:26
Yakin Kasar Ukrain Yana Kara Ruruta Wutar Matsalar Karancin Abinci A Duniya

Hukumar Noma da samar da Abinci na majalisar dinkin duniya FOA ta bayyana cewa yakin kasar ukrain da Rasha ya kawo cikas sosai a bangaren samar da Abinci da mana fetur da kuma takin zamani, wanda haka ya kara jefa miliyoyin alummar duniya musamman nahiyar Afrika da kuma kokarin da kungiyoyin agaji suke yin a ganin sun taimaka musu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ta ci gaba da cewa lamarin yana da ban tsoro sosai, idan ba’a yi taron dangi wajen ganin shawo kan matsalar ba, to za’a fusakanci mummunan bala’I ga bil Adama , don haka an tsara za’a taimaki mutane miliyon 1.93 nan da watanni 6 masu zuwa a yankunan karkara domin hana kara Ta’azarar matsalar yunwa a kasashen Habasha sumaliya da kuma kasar Kenya

Kididdigar farashin kayan abinci da hukumar ta fitar a duniya ya nuna cewa farashin kayayyakin bukatun yau da kulluma sun yi tashin gwaron zabi da ba’a taba gani ba, tun a watan fabareru zuwa maris. Inda a duk wata ya karu da kaso 12.6 cikin dari,

Hauhauwan farashin ya samo asali ne sakamakon tashin farashin hatsi da man girki saboda tasirin yakin kasar Ukrain da Rasha, domin su ne kasahen da ke samar da mafiyawancin Alkama da masara, da man girki daga furanni, da kuma takin zamani da kasar Rasha ke samarwa.

342/