17 Mayu 2022 - 19:28
​Iraki: Dubban Mutane Ne Suke Kwance A Asibitocin Kasar Sanadiyar Hadarin Yashi

Dubban mutane a kasar Iraki suna jinya matsalolin numfashi a asbitocin kasar Iraki sanadiyyar hadarin Yashi wanda mamaye samaniyar larduna da dama a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shafin yanar gizo na Monito na labarai ya nakalto Saiful Badar kakakin ma’aikatar kiwon lafiya na kasar yana cewa akalla mutane 4000 ne suka jinya a asbitocin kasar a halin yanzu sanadiyyar shakar gurbataccen iskar.

Labarin ya kara da cewa wannan shina hadarin yashi na 8 da ya fadawa yankunan daban daban na kasar Iraki a cikin wannan shekara. Sannan hadarin ya shafi lardunan Bagdada babban birnin kasar, Najaf, Sulaimaniyya da kuma yankun kurdawan kasar.

Labarin ya kara da cewa mutum guda ne ya rasa ransa ya zuwa yanzu sanadiyyar shakar kuran da hadarin yake daukowa tare da shi.

Sauyin yanayi da karancin ruwan sama na daga cikin matsalolin da suke haddasa hadarin yanshin.

342/