15 Mayu 2022 - 16:31
Iran Zata Haka Karin Danyen Man Fetur A Lokacinda Farashinsa Yake Kara Sama A Kasuwanrsa Ta Duniya

A dai-dai lokacinda ake kammala kasuwar baje koli na kayakin haka da sarrafa man fetur da Gas nan birnin Tehran, wasu majiyoyi sun nakalto gwamnatin kasar Iran na shirin kara yawan man fetur da zata sayar a kasuwannin duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kamfanonin kere-keren kayakin haka da sarrafa danyen man fetur 1200 ne na cikin gida sannan wasu 40 daga kasashen waje ne suka halarci kasuwar baje kwolin kayakin haka da sarrafa man fetur da gas a nan Birnin Tehran.

Labarin ya kara da cewa kafin takunkuman tattalin arziki na zaluncin da gwamnatin Amurka ta dorawa kasar Ira a shekara ta 2018 dai, Iran tana daga cikin kasashen da suka fi ko wace kasa sayar da mai da iskar gas ga kasashen waje a duniya.

Amma bayan takunkuman da gwammnatin shugaban shugaban kasar Amurka ta dorawa kasar hakar man ya rage zuwa ganga miliyon biyu kawai a yini.

Har’ila yau a wani bangare kuma takunkuman tattalin arzikin sun tilastawa kasar samar da duk kayakin da take bukata na haka da sarrafa man fetur da gasa daga cikin gida, saboda bata samun ingantattun kayakin aiki daga waje saboda takunkuman.

Amma a halin yanzu Iran tana da fasaha da kuma ilmin samar da duk kayakin da take bukata nah aka da sarrafa man fetur da iskar gasa kirar cikin gida.

Sannan tana da ikon hako mai da iskar gas daga kan tutu ko cikin ruwa. Don haka bata bukatar taimakon kasashen waje don yin wadannan ayyuka.

342/