21 Afirilu 2022 - 20:41
Dakarun Gwagwarmayar Falasdinu Sun Harba Makamin Roka A Yankunan Isra’ila

Rahotanni da suka fito daga yankin falasdinu sun sun bayyana cewa an jin karar harba maman roka zuwa yankuna Isra’ila a matsayin martani kan ci gaban da kai hare-haren a yankunan falasdinawa da ta mamaye.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Majiyar labaran Chenne 13 na HKI ta bayyana cewa kimanin yahudawa 4 ne suka jikkata sakamakon harin da aka kai, sai dai jiragen yakin HKI sun kai hari a kudancin Gaza,

Kakakin kungiyar palastinian people Resistan committees Abu mujahid ya fadi cewa a daen jiya laraba sun dauki sabbin matakai na dakile hare-haren da Isra’ila ke kai wa. Ko a kwanakin baya ma kungiyar ta sha alwashin mayar da martani kan hare-haren na Isra’ila a yankin Gaza

Ana sa bangaren kakain ma’aikatar harkoki wajen Iran Saeed khateb zade yayi tir da hare-haren rashin tausayi da Isra’ila ke yi a yankunan palasdinu , yace ya kamata musulmi su hada kai domin goyon bayan falasdinawa da Isra’ila ke zalunta.

342/