Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wani babban jami’in yan sanda a kasar ya fadi cewa jami’an su sun yi amfani da tanakar ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa daliban jami’a da suke zanga-zanga a garin kandy, yace yawansu yakai 750 sai dai ya zuwa yanzu ba’a kama ko daya daga cikinsu ba.
Shugaban kasar Gotabaya rajabaksa ya danar da dokar ta baki a fadin kasar bayan tsibirin dake tekun indiya ya fsukanci matsalar hauhuwar farashin kayan masarufi , kuma ta yi hakan ne a cewarta domin hana yaduwar zanga-zangar a sauran sassan kasar,
Wasu masu sukar manufofin gwamnatin kasar sun bayyana cewa toshen matsalar kasar dadden abu ne musamman rashin yin amfani da tattalin arzikin kasar ba yadda ya dace ba, daga gwamnatin da ta gabata ta yi, wanda ya jawo babban gibi a kasafin kudi da kuma karancin kudade a lalitar gwamnati.
Gwamman shuwagabannin yan adawa ne suka yi zanga-zanga a kusa da dandalin yanci dake kasar kusa da inda yan sanda suka kafa sansaninsu, kuam sun rika rere taken cewa ku koma Gida. Shugan yan adawa a kasar yace ba su amince da dokar ta baci da ma sauran matakan matsain lamba da aka sanya ba.
342/