20 Maris 2022 - 22:11
AU : Ana Samun Ci Gaba A Fannin Ajandar Dunkulewar Nahiyar Afrika

Wani sabon rahoton da Tarayyar Afrika (AU) ta wallafa, ya bayyana cewa, dunkulewar nahiyar Afrika ya zarce matsakaicin mataki, inda kungiyoyin raya tattalin arzikin yankunan nahiyar ke samun nasarori a wannan bangare.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sabon rahoton kan dunkulewar Afrika ya nuna cewa, kungiyar EAC mai raya tattalin arzikin gabashin Afrika da takwararta ta yammacin Afrika wato ECOWAS, da kasuwar bai daya ta gabashi da kudancin Afrika COMESA, sun taka rawar gani a fannin dunkulewar harkokin cinikayya, inda suka samu makin da ya haura kaso 75 cikin 100.

Rahoton na bana, wanda ya yi duba musamman kan zirga-zirgar mutane a matsayin jigon dunkulewar, ya nuna cewa, matsakaicin ci gaban da kungiyoyin yankuna suka samu wajen aiwatar da matakin zirga-zirgar jama’a ba tare da shinge ba na kan matsakaicin mataki na 0.68 idan aka auna tsakanin 0 zuwa 1.

Har ila yau, rahoton ya ce kungiyar ECOWAS da EAC sun yi wa sauran kungiyoyin yankunan zarra a fanin zirga zirgar jama’a cikin yanci, inda makin ECOWAS ya kai kaso 100 yayin da na EAC ya kai kaso 96.

Makin sauran kungiyoyin raya tattalin arzikin yankunan nahiyar a wannan fanni, ya tsaya ne kan kasa da kaso 65.

342/