Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A ranar laraba da ta gabata ce aka saki wasu mata biyu masu shaidar zaman yan kasar Birtaniya da Iran wato Nazanin Zagari da Annosheh Ashoori inda suka isa kasar Birtaniya bayan da suka kwashe shakeru 6 suna tsare a gidan kurkuku a Iran,
Ana sa bangaren babban Jami’in diplomasiyyar Iran ya jinjinawa kasar Oman game da muhimmiyar rawa mai ma’ana da ta taka wajen warware batutuwan da suka hada da batun fursunoni da ake tsare da su kan batun tsaro.
Shi ma ministan harkokin wajen kasar Oman Sayyid Badr Al-busaidi ya jaddada game da muhimmancin ci gaba da kyautatuwar dangantaka tsakaninsu kuma ya bayyana fatansa na ganin an dauki mataki na karshe a tattaunawar Vianna da ake yi na cirewa Iran takunkumi nan ba da jimawa ba.
342/