Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jagoran wanda ya dasa bishiyoyi biyu, ya kara da cewa; Shuka bishiya, aiki ne na addibi, na juyin juya hali, sannan kuma a lokaci daya kare muhalli.
Har ila yau jagoran ya bayyana cewa; sare dajuka da gurbata muhalli suna cin karo da manufofin kasa, haka nan kuma sare bishiyoyi dmin ayi amfani da su wajen gine-gine, yana cutar da al’umma,sai idan ya zama lalura.
Jagoran juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma ce; Batun kare muhalli yana daya daga cikin muhimman batutuwa na kasa, yana kuma mai kara da jaddada wajabcin kare ruwa da kasa da suke a matsayin wasu taskoki na kasa. Jagoran ya kira yi mahukunta da su yi aiki da shawarwarin da kwararru a wannan fagen su ka gabatarwa.
Dangane da kare gandun daji, Imam Ayatullah Sayyid Aki Khamnei ya yi kira da hana farauta ba isa ka’ida ba, ya kuma kira yi ma’aikatar gonad a ta hana lalata gonaki da mayar da su wasu abubuwan daban.
342/