Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Har ila yau Sayyid Nasrullah ya yi gargadi cewa makomar rikicin Rasha da Ukrain yana da matukar hatsari ga duniya baki daya idan aka yi la’akari da abin da ke faruwa a kasa.
Bayanan nasa yana zuwa ne bayan kalamai masu harshen damo da kafafen watsa labarai na kasashen turai suke yadawa kan rikicin rasha da Ukrain da ya jawo yin tir daga kasashen duniya.
Daga karshe ya sanya alamar tambaya game da irin matakin da duniya ta dauka lokacin da Amurka ta mamaye kasar Afghanistan da kuma wanda ta nuna bayan harin soji da kasar Rasha ta kai a kasar Ukrain . yace duniya tana girmama mai karfi ne kawai amma tana yin gum da baki kan taifukan da Amurka take tafkawa.
342/