23 Faburairu 2022 - 13:30
HRW Ta Nemi A Daina Kasuwanci Da Yankunan Da Isra’ila Ta Mamaye

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Human Rights Watch, ta bukaci duniya musamman kasashen turai dasu daina mu’amular kasuwanci da yankunan dake karkashin mamayar Isra’ila.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta HRW, ta ce ci gaba da kasuwanci da yankunan da Isra’ila ta mamaye tamakar cin zarafin dan adam ne, kuma dole a kawo karshensa.

A game da hakan ne kungiyar ta bukaci kwamitin kungiyar tarayyar turai, da ya haramta duk wani kasuwanci da yankunan da dake karkashin mamayar Isra’ila musamman na Faladinawa, saboda hakan a cewarta tamakar laifukan yaki ne.

Wasu alkalumma da bankin duniya ya fitar a shekarar 2012, sun nuna cewa kayayacin kasuwanci da kungiyar EU, ke shigar dasu zuwa yankunan falasdinawa da Isra’ila ta mamaye sun kai kusan na Dala Miliyan 300.

342/