Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Faransa ta ce dakarun na ta da na turai za’a mayar da su kasar Nijar inda daga cen zasu jagoranci ayyukan yaki da ta’addanci a yankin na Sahel.
Shugaba Macron ya sanar da hakan ne a birnin Brussels inda yake halartar taron kungiyar tarayyar Afrika da kuma takwararta ta turai.
Matakin na faransa dai bai zo da mamaki ba duba da takun sakar da ake fuskanta a baya baya nan tsakanin sojojkin dake rike da mulki a Malin da kuma kuma mahukunatan Paris, sai kuma takaddamar dake tsakanin bangarorin game da kasancewar sojojin hayar Rasha na Wagner da faransa ta kiyasta sun kai 1,000 a Mali.
A kwana baya dai Mali ta kori jakadan faransa daga kasar, domin nuna bacin rai game da wasu kalamai da ta danganta da na batanci da ministan harkokin wajen faransar Jean Yves Le Drian , ya firta ga mahukuntan rikon kwaryar soji na Bamako.
An jima kuma da jama’ar kasar Mali ke zanga zangar nuna kin jin sojojin kasashen yamma musamman na faransa a kasar.
342/