2 Faburairu 2022 - 19:10
Kungiyar Malaman Ahlul Baiti (AS) Ta Yi Ta’aziyyar Rasuwar Ayatullah Safi Golpayegani.

Kungiyar malaman Ahlul Baiti (AS) ta aike da sakon ta'aziyyar rasuwar Ayatullah Safi Golpayegani.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - habarta cewa, bayan rasuwar Ayatollah Safi Golpayegani, babban mai kula da harkokin shi'a, kungiyar hadin kan malaman kasar Turkiyya (Ahladar) ta fitar da sakon ta'aziyya.

Matanin wannan sakon shine kamar haka:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

Ayatullah Khamenei, majibincin Lamurran Musulman Duniya Dz

Muna mika ta'aziyyarmu na rasuwar Ayatollah Safi Golpayegani ga Jagoran juyin juya halin Musulunci, da makarantun hauza da kuma iyalan mamacin. Allah madaukakin sarki ya daukaka darajar wannan maraji'in mai girma, kuma ya karawa wannan shugaba mai hikima tsawon lokaci, kuma inuwarka ta dawwama a kanmu da dukkanin musulmin duniya baki daya.

Assalamu alaikum wa rahmatullh Wabarakatuh

Gamayyar Malamai Ahlul Baiti
Turkiyya - Istanbul

342/