Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Mondli Gungubele wani minista a fadar shugaban kasa yana fadar haka a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa gwamnatin ta dauki wannan matakin ne bayan taron majalisar ministocin kasar inda aka tattaunawa irin sauye-sauyen da za’a gabatar bayan an yi wa mutanen masu yawa alluran riga kafin cutar.
Gungubele ya kara da cewa a halin yanzu wadanda suka kamu da cutar kuma suna dauke da alamunta to zasu killace kansu na kwanaki 7 ne maimakon kwanaki 10 a baya. Har’ila yau an yi maganar sake bude makarantu ba tare da la’akari da dokar nisantar juna na mita guda tsakanin mutane a ajujuwa ko wuraren taro ba. Mutane miliyon 3.6 ne suka kamu da cutar Covid 19 a Afirka ta Kudu tun bayan bullatar a shekara ta 2020, inda 95,093 daga cikinsu suka rasa rayukansu ya zuwa yanzu.
342/