30 Janairu 2022 - 17:06
​Siriya: Amurka Ta Canzawa Mayakan Daesh Wuri Daga Hasaka Zuwa Dayr-Zur

Rahotanni da suke fitowa daga kasar Siriya sun bayyana cewa sojojin Amurka a arewacin kasar sun canzawa fursinonin mayakan kungiyar Daesh wuri daga gidan yarin Al-Sina’a na Hasaka zuwa Dayr Zur.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Rasha ya bayyana cewa fursinonin Daesh 750 aka canzawa wuri, sannan daga cikinsu akwai kwamandojinsu. Labarin ya kara da cewa fursinonin yan kasashen larabawa ne da kuma wasu kasashen turai.

Jakadan kasar Siriya a MDD Bassam Sabbagh ya bayyana cewa Amurka ta yi haka ne don ta samarwa kanta uzurin ci gaba da kasnacewar sojojinta a arewacin kasar Siriya. Don haka yayi kira ga kasashen Amurka da Turkiyya da su fidda sojojinsu daga kasar.

Amurka ta yi aikin canzawa mayakan na Daesh wuri ne tare da taimakon kungiyar Kurdawa ta 'Syrian Democratic Forces (SDF)' wadanda suke samun goyon bayan Amurka wajen satar man fetur na kasar ta Siriya a yankin da kuma ci gaba da samar da tashe tashen hankula a yankin.

342/