Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministar Kuɗi da Tsare-Tsare Zainab Ahmed Shamsuna ce ta bayyana hakan ranar Laraba jim kaɗan bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa ta Ƙasa.
Ta ƙara da cewa Najeriya na buƙatar ta ƙara naira tiriliyan biyu da rabi a cikin kasafin kuɗinta na 2022 don biyan kuɗin tallafin yayin da za ta gabatar da buƙatar gyaran ga 'yan Majalisar Tarayya.
"A 2022, sakamakon ƙaruwar farashin mai a kasuwar duniya zuwa dala 80 kan kowace ganga ɗaya a yanzu, sannan kuma ƙiyasin NNPC ya nuna cewa ana shan litar mai miliyan 6.5 a kullum a Najeriya, hakan zai sa mu samu ƙarin naira tiriliyan uku a 2022," in ji ta.
A cewar ministar, gwamnatin tarayya na kashe kusan naira biliyan 270 a kowane wata wajen biyan tallafin mai.
Ta ƙara da cewa a yanzu an tanadi biliyan 443 ne kawai a kasafin kuɗi na 2022, wanda a da aka tsara za a biya daga Janairu zuwa watan Yuni kawai.
Majalisar ta duba buƙatar kamfanin mai na NNPC sannan ta umarci Ma'aikatar Kuɗi da Tsare-Tsare da ta fara tattaunawa da 'yan majalisa don yi wa kasafin kuɗin kwaskwarima.
342/