Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Raeisi ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da ministan harkokin wajen kasar Togo Robert Dussey a yau litinin, inda ya ce a karkashin sabuwar gwamnatin Iran, kasar za ta ci gaba da kara bunkasa dangantakar tattalin arziki, kasuwanci da siyasa da kasashen Afirka.
Ya ce kasashen yammacin duniya sun fi neman yin mulkin mallaka da kuma amfani da kasashen Afirka domin cimma burinsu, kuma a halin yanzu suna biyan bukatun kansu a nahiyar ta fannoni daban-daban, bisa la'akari da dimbin arziki da Allah ya huwace wa kasashen nahiyar Afirka.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Togo ya ce kasarsa na da burin kulla cikakkiyar alaka da Iran, domin karfafa kasashen biyu wajen cimma moriyar juna.
Dussey ya yi Allah wadai da takunkuman da kasashen yamma suke kakabawa kasashe masu cin gashin kansu, wadanda suka zabi su rayu a cikin 'yanci na siyasa.
342/