21 Janairu 2022 - 21:24
​Chadi: Gwamnati Ta Saki Wasu Daga Cikin “yan Tawaye Da ‘Yan Adawa Da Nufin Samun Sulhu

Gwamnatin Chadi ta saki wasu 'yan tawaye da jigajigan 'yan adawa 22 da ake tsare da su bisa zargin cin amanar kasa, wanda ke zama kason farko cikin fursunonin da shugaban kasar ya yi wa afuwa domin sulhunta ‘yan kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mutanen 22 na daga cikin ‘yan tawaye da jigajigan ‘yan siyasa kimanin 296 da shugaban mulkin sojin kasar Mahamat Kaka Idris Deby ya sanar da yi musu afuwa a karshen watan Nuwamba.

Yin afuwar dai na daya daga cikin sharuddan da 'yan adawa suka gindaya domin shiga tattaunawa kan makomar kasar mai fama da rikici.

Shugaba Mahamat, mai shekaru 37, wanda ya karbi ragamar mulkin Chadi bayan da aka kashe mahaifinsa Idriss Deby Itno cikin watan Afrilun bara a fagen daga, ya bukaci tattaunawa da ‘yan tawaye masu dauke da makamai.

Wannan ne ya sa ‘yan tawayen suka gindaya wasu sharudda, daga ciki suka bukaci sakin daukacin fursunonin da aka kama a yaki, da kuma yin afuwa ga ‘yan adawa tare da maidawa ‘yan tawaye dukiyoyin su da gwamnati ta kwace.

342/