8 Janairu 2022 - 18:07
Hamas Ta Jadda Aniyarta Ta ci Gaba Da Yaki Da Isra’ila

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmya ta Hamas ta jaddada game da hakkinta na ci gaba da yaki da mamayar Isra’ila , ta ce laifukn da Isra’ila ta aikata kan alummar falasdinu ya wuce misali, kuma dole a hukumta shuwagabannin da sojoji Isra’ila kan laifuka yaki da suka tafka da kuma kisan kare dangi da suka yi kan mata da yara kanana,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Haka zalika kungiyar ta jaddada alkawarin da ta dauka na daukar fansar jinin shahidai , kuma sun sha alwashin ci gaba da bin hanyar gwagwarmaya har sai an dawo da dukkan yankunan falasdinawa da Isra’ila ta mamaye, ta koresu da ga ciki

Daga karshe ta soki Isra’ila game da ci gabe da rike gawawwakin shahidai sama da 253 a wasu kabaruruka na gama gari fiye da shekaru 10 , tare da bayyana haka a matsayin laifukan yaki, kuma ta ce babu ja da bawa game da batun dawo da gawawwakin shahidai da take rike da su.

342/