5 Janairu 2022 - 14:25
​Koriya Ta Arewa Ta Harba Wasu Makamai Masu Linzami

Koriya ta arewa ta harba wasu makamai masu linzami zuwa tekun gabashin yankin, kamar yadda rahotanni daga Koriya ta kudu suka nakalto a yau Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rahotanni daga yankin sun ce ta harba makaman ne mai cin gajeren zango ba tare da yin wani karin haske ba.

Wannan shi ne karon farko da Koriya ta arewan ta yi gwajin makamai masu linzami a sabuwar shekarar nan ta 2022 da muka shiga.

Gwaji na baya bayan nan da ta gudanar shi ne na ranar 19 ga watan Oktoban bara a lokacin da koriyar ta Arewar ta yi gwajin sabon samfurin makami mai linzami dake gudu a tsakiyar teku.

342/