Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Tribune ta Najeriya ta nakalto Femi Adesina yana fadar haka a wani shirin mai suna ‘Sunday Politics’ ta tashar talabijin ta ‘Channel News’ a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja.
Adesina ya tabbatar da cewa wasu daga cikin mataimaka shugaban kasa wadanda suke aiki tare da shi sun kamu da cutar, gaskiya ne, amma baa bin damuwa bane.
Labarin ya kara da cewa babban mai bawa shugaban kasa shawara kan al-amuran yada labarai Malam Shehu Garba ya tabbatar da cewa ya kamu da cutar, amma ya ce, tun da ya riga ya yi alluran riga kafin har guda 3, shi bai ji wata alama ta kamu da ita, sai bayan da likitoci suka fada masa ya kamu da ita. Sannan a halin yanzu ma yana gudanar da harkokinsa da kansa a kebe, kamar yadda aka umurce shi ya yi.
Sai dai daga cikin ministoci, ministan watsa labarai Mr Lai Muhammad ya karyata cewa ya kamu da cutar, ya kuma bukaci kafafen yada labia na zumunta wadanda suka fara bada labarin su nemi afwarsa.
342/