22 Disamba 2021 - 13:19
Dole Isra’ila Ta Fice Daga Tuddan Golan Da Dakatar Da Kai Hari Siriya.

Zahara Irshadi wakiliyar Iran ta din din din a majalisar dinkin duniya ta yi kira ga kwamitin tsaro na majalisar da ya tilastawa Isra’ila ta kawo karshen mamaye toddan Golan da ta yi da kuma dakatar da kai hare-hare kan kasar Siriya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Ta ce: “ kasar Siriya tana da hakkin hare kanta daga duk wani wuce gona da Irin Isra’ila a kowanne lokaci a kuma wajen da ta zaba, don haka ci gaba da mamaye wani yankin kasar siriya da sojojin kasashen waje suka yi, keta dokokon kasa da kasa da kudurorin majalisar dinkin duniya ne

Har ila yau ta ce :” dole ne dukkan sojojin kasashen waje da ba’a gayyace su ba su fice daga kasar Siriya ba tare da wani wani sharadi ko jinkiri ba.

Rahoton da kafafen watsa labaran kasar Amurka suka fitar a baya bayan nan, ya nuna yadda aka kashe gwamman fararen hular kasar siriya da suka hada da manoma mata da mazauna karkara da sojojin Amurka suke yi, kuma wannan abin ayi tir ne da shi, kuma wannnan ya nuna irin bukatar da ake da ita na ficewar su daga siriya cikin gaggawa.

342/