Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - A rahoton da gidan rediyon Faransa ya bayar, matakin kungiyar Kwadagon na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta Ayuba Wabba bayan taron majalisar zartaswar koli da suka yi a Abuja a karshen mako.
A cikin watan Nuwamban da ya gabata, Ministar kudin Najeriya Zainab Ahmed, ta bayyana shirin gwamnatin tarayyar Najeriya na cire tallafin man fetur, wanda ta ce za a maye gurbinsa da bayar da tallafin sufuri na naira dubu biyar ga masu karamin karfi akalla su miliyan 40 a fadin Najeriya, domin rage musu radadin tasirin cire tallafin man.
Sai dai duk da haka kungiyar NLC ta sha alwashin jagorantar zanga-zanga a dukkan jihohin Najeriya 36 a ranar 27 ga watan Janairun da ke tafe, yayin da kuma a birnin Abuja za ta yi gangamin a ranar 1 ga watan Fabarairu.
Batun cire tallafin mai a Najeriya ya sake tasowa a baya bayan nan ne, kasa da mako guda bayan da Hukumar ba da Lamuni ta Duniya IMF ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta cire tallafin na man fetur domin karkata kudaden da take zubawa zuwa ga ayyukan raya kasa, inda shugaban kamfanin man NNPC Mele Kyari ya ce farashin man na iya kaiwa naira N320 zuwa N340 a kan kowace lita guda daga shekarar 2022 mai kamawa.
Yayin da yake gabatar da jawabi a Abuja, Kyari yace tabbas babu abin da zai hana cire tallafin man a shekara mai zuwa, domin kuwa dokar da ake amfani da ita wajen biyan tallafin za ta daina aiki daga karshen watan Fabarairu mai zuwa.
342/