19 Disamba 2021 - 13:14
​Iran: An Fama Yiwa ‘Yan Gudun Hijira Rigakafin Covid 19

Manistan harkokin cikin gida na kasar Iran ya ce gwamnatin kasar tana da shirin yiwa dukkan ‘yan gidun hijira da suke cikin kasar alluran riga kafin cutar Covid 19.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - na kasar Iran ya nakalto Ahmad Wahidi yana fadar haka ya kuma kara da cewa tuni an yiwa wasu 'yan gudun hijirar, sannan sauran ma za yi masu nan ba da dadewa ba.

Banda Wahidi ya bukaci duk wanda zai shigo kasar daga kasashen waje ya tabbatar ya yi alluran riga kafin cutar ta Covid19 don tsari da lafiyansa da kuma ta sauran ‘yan kasa.

Fiye da shekaru 40 da suka gabata ne kasar Iran take daukar bakwancin ‘yan gudun hijira kimani miliyon 4 daga kasar Afganistan. Banda haka bayan ficewar Amurka daga kasar ta Afgansitan a cikin watan Augustan da ya gabata dubban yan kasar da Afgansitan ne suka kwarara zuwa cikin kasar ta Iran.

Daga karshe ministan ya bukaci mutane su yi amfani da dokokin hana yaduwar cutar ta Covid 19 sannan su kula da tsabtar jikinsu don kare kansu da wadanda suke tare da su daga kamuwa da cutar.

342/