10 Disamba 2021 - 18:50
​Yemen: Mata Akalla 2,400 Ne Suka Mutu Sanadiyar Ruwan Boma-Boman Kawancen Saudiya A Kan Kasar

Kamfanin dillancin labaran Yemen SANA ya nakalto rahoton kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Intisaaf” ta kasar tana bada rahoto a safiyar Jumma’a dangane da take hakkin mata a kasar tun bayan mamayar da sojojin kasar Saudiya da kawayenta suka yi wa kasar a 2015.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Rahoton ‘Intisaaf’ ya kara da cewa daga ranar 26 ga watan Maris na shekara ta 2015 zuwa 8 ga watan Dicemba da muke ciki, mata 2,412 suka rasa rayukansu sanadiyar ruwan boma-bomai a kanwa wanda jiragen yakin Saudiya da kawayenta suka yi a kan kasar. Sannan wasu 2,825 kuma suka ji rauni.

Rahoton ya kara da cewa matan da suke karkashin ikon sojojin mamaya a kudancin kasar suna fuskantar cin zarafi har zuwa kashi 63% daga cikinsu.

Har’ila yau kungiyar ta kara da cewa mutane kimani 65,000 suke fama da cutar kansa a kasar sanadiyyar yakin, da dama daga cikinsu mata ne. Sannan wasu marasa lafiya kimani 12,000 suke bukatar aikin tiyata na koda a kasashen waje amma kofar ragon da aka yiwa kasar ya hana hakan.

Daga karshen kungiyar ‘Intisaaf’ ta kammala da cewa, mata kimani 1,200,000 suke fama da karancin abinci mai gina jiki, a kasar da dama daga cikinsu mata ne masu juna biyu. A ko wace shekara mata 8,000 suke mutuwa saboda kellace kasar da Saudiya ta yi. Sannan kasha 70% na magungunan da ake bukata a kasar ba’a samunsu.

342/