9 Disamba 2021 - 16:41
Yau Ake Sake Komawa Sabon Zagayen Tattaunawar Vienna

Yau Alhamis ake komawa tattaunawar neman farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran, bayan da bangarorin da batun ya shafa suka koma gida somin shawarwari a makon da ya gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Kusan dukkan bangarorin sun tabbatar da komawa bakin tattaunar ta Vienna, da a yayin ta Iran ke fatan za’a dage mata takunkuman da ta Amurka ta kakaba mata.

A makon da ya gabata dai Iran, ta gabatarwa da bangarorin daftarin shawarwarin neman cire mata takunkuman da tsohuwar gwamnatin Amurka ta kakaba mata a 2018.

Ana kallon wannan zagayen a matsayin wata dama ta karshe a yunkurin farfado da yarjejeniyar ta 2015.

342/