8 Disamba 2021 - 13:13
Jirgin Helikobta Ya Yi Hatsari Dauke Da Babban hafsan Sojin Indiya

Rundinar sojin Indiya, ta sanar da cewa wani jirgin saman mai saukar ungulu ya fadi dauke da babban hafsan tsaron kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Sanarwar da rundinar ta fitar a shafinta na Tuwita, ta ce jirgin helikobta kirar Mi-17V5 na IAF, ya fada dauke da janar Bipin Rawat.

Lamarin ya faru ne a yankin Tamil Nadu dake kusancin kasar a kusa da Coonoor a Tamil Nadu a cewar rundinar.

342/