5 Disamba 2021 - 16:24
Iran : Fashewar Da Akaji A Natanz, Gwaji Ne Na Makaman Garkuwa Daga Hare-haren Sama

Rundinar sojin saman Iran, ta yi karin haske game da rahotannin fashewar data auku a birnin Natanz wanda ya kunshi tashar nukiliya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Kwamnadan rundinar ya fada a gidan talabijin din kasar cewa, fashewar da aka ji, wani gwaji ne na auna saurin makamman kare kai daga hare haren sama a yankin na Natanz.

Rundinar ta ce ta harba wani makami mai linzami a saman binrin Natanz domin gwada saurin makamin kariya daga hare haren sama, kuma babu wani abun damuwa.

Lamarin ba shi da wata alaka da tashar nukiliyar Natanz, kuma an saba yin irin wannan gwajin tare da hadin guiwar duk bangarorin da batun ya shafa domin auna irin wadanan makamman na kariya dake a yankin.

342/