3 Disamba 2021 - 16:11
Vienna : Iran Ta Gabatar Da Daftarin Shawarwarin Cire Mata Takunkumi

Iran ta baiwa bangarorin da suka kulla yarjejeniyar nukiliyar kasra ta 2015 daftarin takardun da suka yi bayani dalla-dalla kan shawarwari da matsayar ta kan cire takunkumin da Amurka ta kakaba mata bayan ficewa daga yarjejeniyar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Daftarin ya kuma kunshi jerin matakan nukiliyar da Tehran ta dauka, a matsayin maida martani kan ficewar Amurka daga yarjejeniyar.

Da yake zantawa da wakilin tashar talbijin din Press TV a babban birnin kasar Austriya ranar Alhamis, mai jagorantar tawagar Iran a tattaunawar Ali Baqeri-Kani ya ce an mika wasu daftari guda biyu da aka kammala ga bangarorin P4+1 da suka hada da Faransa da Birtaniya da Jamus da Rasha da kuma China.

Ya kara da cewa, abubuwan da ke cikin daftarin sun hada da dukkan shawarwari da kuma matsayin tawagar ta Iran, kuma a cewarsa yanzu Iran na dakon jin ta bakin bangaren.

A ranar Litini ne aka koma bakin tattaunawar ta Vienna, da zumar farfado da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran a 2015, wacce AMurka ta fice a ciki a 2018, tare da kakabawa Iran jerin takunkumai.

Iran ta ce cire mata jerin takunkuman shi ne abunda ta dukufa akan shi a yayin tattaunawar da ta shiga kwana na hudu a Vienna.

342/