Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ana sa bangaren Mohammad Islami ya fadi cewa: “ babban abin da ke da muhimmanci game da batun dake tsakanin Iran da hukumar nukiliya ta duniya kan abin da ya shafi fasaha ne, don haka yana fatar hukumar ba za ta tasirantu da batutuwa na siyasa da makiya kasar Iran suke amfani da su wajen shafawa shirin nukiliyar Iran kashin kaji ba.
Majalisar shawarar musulunci ta kasar Iran ta takaita wuraren da sakataren hukumar IAEA zai kai cibiyoyinta na nukiliya domin mayar da martani game da janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a shekara ta 2018 kana kuma ta kakaba mata takunkumi mafi muni a tarihi.
342/