22 Nuwamba 2021 - 13:16
​Sabon Babban Sakataren Kungiyar Kasashen Musulmi Ya Fara Aikinsa A Hukumance

Sabon babban sakataren kungiyar kasashen musulmi dan kasar Chadi ya fara aiki a ofishinsa a hukumance.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shafin yanar gizo na OIC ya bayar da bayanin cewa, Hussein Ibrahim Taha ya fara aiki a matsayinsa na babban sakataren kungiyar kasashen musulmi a hukumance.

A zaman taro karo na 47 na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da aka gudanar a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, aka ayyana shi a matsayin sabon sakataren janar na kungiyar.

An haifi Hussein Ibrahim Taha a shekarar 1951 a birnin Abshi na kasar Chadi, inda ya yi karatun firamare da sakandare a kasar Chadi.Baya ga aikin jakadanci da ba da shawara, an zabe shi a matsayin ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na kasar Chadi a shekarar 2017, kuma an nada shi mai baiwa shugaban kasa shawara a shekarar 2019.Sauran mukaman nasa sun hada da jakadan Chadi a Faransa, Spain, Portugal, Girka da kuma Vatican. Ya kuma kasance babban mai ba da shawara ga ofishin jakadancin Chadi a Saudiyya.

Sabon Sakatare Janar na Kungiyar Hadin Kan Musulunci, wanda ya kware a harsunan Faransanci, Larabci da Ingilishi, ya karbi sabon mukaminsa na Sakatare Janar na Kungiyar Hadin Kan Musulunci ne a matsayin magajin Yusuf bin Ahmad Al-Uthaymeen.

342/