19 Nuwamba 2021 - 10:40
Ayatullah Mujtahed Shabestari Ya Yi Bankwana Da Duniya + Tarihin Rayuwa

Ayatullah Muhsen Mujtahed Shabestari, tsohon shugaban majalisar koli ta Ahlul-baiti ta duniya (AS) yayi wafati.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) - ABNA- kawo ya labarin cewa, Ayatollah Mohsen Mujtahid Shabestari, mamba ne a majalisar koli ta Ahlul-baiti ta duniya (AS) kuma daya daga cikin jagororin jihadi da ijtihadi. , ya karba kira ubangiji yana da shekara 84.
Ya Kasance shekarun baya bayan nan bayan karewar wakilcin Jagoran juyin juya halin Musulunci a birnin Tabriz, yana rayu ne a birnin Tehran kuma an kai shi asibitin Imam Husaini (AS) ne sa’a daya da ta gabata sakamakon bugun zuciya Amma magungunan ba su yi tasiri ba ya inda yayi wafati.
Ayatullah Mujtahed Shabestari yana daya daga cikin daliban Imam Rahel (as) kuma dan gwagwarmayar Harkar Musulunci wanda bayan nasarar juyin juya halin Musulunci yana rike da ayyuka kamar wakilcin majalisar shawarar Musulunci.
A shekara ta 1373 (Hijri Shamsy) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya zabi Ayatullah Mujtahed Shabestari a matsayin Limamin Juma'a na Tabriz kuma ya dauki wannan gagarumin nauyi har zuwa watan Khurdad 1396.
Sauran ayyukan da Marigayi Marabauci ya rike su sun hada da shugabancin Majalisar koli ta Majalisar Ahlul-baiti (AS) ta Duniya, limamcin Sallar Juma'a a Tabriz, menba a kungiyar malamai masu gwagwarmaya, kuma ya zamo wakili na lokuta da daman a mutane a majlissar masu kawo wa Rahbar labara kuma ya kasance menba a majalissar tantance ingancin tsari musulunci duka wadannan mukamai suna daga cikin mukaman da marigayin ya rike lokacin rawuwarsa.

Takaitaccen Tarihin Ayatullah Muhsen Mujtahed Shabestari
An haifi Ayatullah "Muhsen Mujtahid Shabestari" dan Ayatullah "Mirza Kazem Mujtahid" a shekara ta 1316 bayan hijira kidayar shamsiyya a birnin "Shabestar".
Ya kammala karatunsa na firamare a garinsu da aka haifeshi yayi sakandare a birnin "Tabriz" a shekara ta 1332Hs Ya tafi birnin jihadi da ijtihadi "Qom" domin karantar ilimin addini.
Bayan ya koyi darassa na muqaddimat da kuma karatun tsakatsaki, ya karanci darul khariji bangaren ilimin fikihu da Usul sannan kuma a gaban manya manyan marajio’I kamar Ayatullah "Burujerdi", "Imam Khomeini" da "Sayyid Mohammad Muhaqqih Damad", "Seyyed Mohammad Reza Golpayegani". da "Mirza Hashem Amoli" Shi (Allah Ya jiqansu) ya samu karatu. A karatun falsafa da tafsiri yana daya daga cikin daliban "Allamah Tabatabai" sannan kuma ya amfana da darussan Akhlaq na Ayatullah "Hussain Fatimy Qummy da Sheikh "Abbas Tehrani".
Malam Mujtahid Shabestari a shekara ta 1351hs. Bisa gayyatar da wasu jama'ar Tehran suka yi masa, ya je wannan birnin ya gabatar da sallolin jam'i, ya koyar da ilimin addini, da shiryar da jama'a a masallacin Talachian.
* Gwagwarmayarsa
Marigayi Mujtahed Shabestari ya kasance daya daga cikin mambobin kungiyar limamai yan gwagwarmaya a birnin Tehran tun farko kafa wannan kungiyar, kuma ya taka rawar gani wajen shirya takardu sanarwa da shirya tattakin da wannan kungiya ta shirya domin yakar gwamnatin azzalumai. Saboda wadannan ayyukan, jami'an SAVAK sun yi ta yi masa sammace da kama shi, amma bayan an sake shi, bai yi watsi da abunda ya saba ba na yakar daular Pahlavi ba.
Daya daga cikin wadannan kame-kamen da aka yi a cikin watan Ramadan na shekarar 1977. An kama shi ne tare da malamai 21 daga Tehran, wanda ya yi mummunan tasiri a kan yankunan daular.
Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Mujtahed Shabestari a ko da yaushe ya kasance aminin Imam Khumaini (RA) kuma sahabin Jagora na gaskiya, kuma yana kan gaba a fagagen kare juyin juya halin Musulunci. Babban abin da ba a mantawa da shi na wannan kasantuwar da tsayin daka shi ne yunkurin da al'ummar kasar da suka yi a ranar 29 ga watan Disamban shekara ta 2009 don nuna goyon bayan juyin juya halin Musulunci da Wilayatul Faqih a birnin Tabriz - kwana daya kafin ranar 9 ga watan Diyah a duk fadin kasar Iran - wanda ya faru da agazawa ta wannan mutumin mai kare juyin juya hali ya jagoranta.

* Mukaman Da Ya Rike
Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci ya jagoranci kwamitocin juyin juya halin Musulunci a gundumar ta 6 ta birnin Tehran, sannan a zagayen farko na zaben majalisar shawarar Musulunci ya wakilci al'ummar Tehran a majalisar. A zango na biyu, na hudu da na biyar, shi ma ya wakilci mutanen Tehran a majalisar shawarar Musulunci.
Al'ummar lardin Azarbaijan ta gabas ne suka zabi Ayatullah Mujtahed Shabestari a matsayin wakili a karo na uku na majalisar kwararrun jagoranci, kuma al'ummar lardin Azarbaijan ta gabas ne sun kara zaben shi a zango na hudu da na biyar na wannan majalisar.
Bayan tafiyar marigayi Ayatullah "Muslim Malakouti" daga Tabriz zuwa Qum a watan Yunin 1995 Jagoran juyin juya halin Musulunci ya nada shi a matsayin wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a lardin Azarbaijan ta Gabas da kuma limamin Juma'a na Tabriz.
A watan Nuwamban shekarar 2012, bayan marigayi Ayatullah “Mesbah Yazdi”, ya zama shugaban majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul-Baiti (AS), wanda ya ci gaba har zuwa watan Oktoban shekara ta 2019.
Ya kuma kasance cikakken memba na Majalisar Dokoki bisa umarnin Jagora.
* Ayyukansa Na Ilimi
Ayatullah Mujtahed Shabestari a lokacin da ya halarci makarantar hauza a birnin Qum da a nan Tehran ya koyar da ilimomin hauza daban-daban.
Ya shafe shekaru 3 yana koyarwa a tsangayar ilimin tauhidi ta jami'ar Tehran, sannan kuma ya koyar da fikihu tsawon shekaru a garuruwan Tabriz da Tehran.
Haka nan kuma ya horas da dimbin malamai da za su yi wa al'ummar musulmi hidima a karkashin kulawar makarantar tauhidi ta Ayatollah Irvani da ke nan Tehran.
Ayyuka da rubuce-rubucen marigayi sun fi yawa a fagagen tafsiri, aqida, fiqihu da Usul: Ciki har da:
- Tafsirin surorin juma'a da munafukai
- Rubutun tafsiri akan surorin Fatiha da ikhlasi
- Abdurraham
-Littafin Tajallin Nur
- Wilat Faqih; Cigaban Waliyyar Imamai (as)
- Rubuta Littafin al'adun jama'a a cikin al'ummar Musulunci

* Wafatinsa
Daga karshe bayan gwagwarmayar rayuwarsa a ranar Laraba 26 ga watan Aban 1400HS (daidai da 11 Rabi’uth Thani 1443AH da 17 ga Nuwamba 2021AD) yana da shekaru 84 da haihuwa, ya amsa gayyatar da aka yi masa, sakamakon ciwon shanyewar jiki da ya yi masa, kuma ya rasu a kasar. birnin "Tehran".

342/