15 Nuwamba 2021 - 16:55
Lavrov : Rasha Za ta Goyi Bayan Cire Wa Iran Takunkumi A Taron Vienna

Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa, Moscow na yin kira da a dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron da za a yi a Vienna a ranar 29 ga watan Nuwamba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Da yake magana da manema labarai a birnin Paris a ranar Juma'a, Lavrov ya ce a karshen ganawar da ministocin harkokin wajen Rasha da Faransa da na tsaro suka yi: "A yayin shawarwarin Vienna, Moscow za ta yi kira da a aiwatar da cikakken tsarin yarjejeniyar Nukiliya da kuma dage takunkumi. "

“Tabbas, wannan ya hada da mayar da Amurka a cikin yarjejeniyar don cika nauyin da ya rataya a wuyanta.

Dangane da tattaunawar da aka yi da ministocin harkokin wajen Faransa game da yarjejeniyar nukiliyar, ministan harkokin wajen Rasha ya ce: “A yayin wannan taro, mun tattauna batun tattaunawar da za’a yi nan gaba kuma muna fatan samun karin hadin gwiwa tsakanin Rasha da Faransa game da wannan batu.

342/