Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto kakakin ‘yansanda na Jihar Gambo Isa, ya na cewa, suna da tabbacin kisan mutane 11 amma mutanen garin sun ce adadin ya kai 13.
Labarin ya kara da cewa ‘yan bindigan sun zo da yawa da misalign karfe 7:15 na yamma, a lokacinda wasu mutane suna masallaci, sai suka bude wuta kan mai uwa da wabi suka kashe mutane 13, wadanda aka yi masu jana’iza a safiyar yau Laraba, inji wani dan garin wanda ake kira Abubakar Bashir.
Mamba a majalisar dokokin jihar Katsana daga yankin Batsari, Jabir Yau Yau ya fadawa Premium times kan cewa ya na da labarin aukuwar lamarin amma ba zai fadi kome ba sai ya je ya ganewa idanunsa abinda ya faru.
Wani dan garin Batsari, mai suna Mukhtar Mamman ya ce ‘yan ta’addan sun dauki sa’o’ii da dama su na cin karensu ba babbaka a garin kafin su tafi da wasu daga cikinsu cikin dajin All..
342/