8 Nuwamba 2021 - 12:10
​Haaretz: Haftar Na Gudanar Da Tattaunawa Da Isra’ila A Asirce Domin Kulla Alaka

Jaridar yahudawan Isra’ila da ake bugawa a cikin harshen Hebrew ta bayar da rahoton cewa, a jiya Lahadi, ɗan Manjo Janar Khalifa Haftar mai ritaya, ya kai wata ziyara a asirce a birnin "Tel Aviv" na Isra’ila a makon da ya gabata, inda ya isar da saƙo daga mahaifinsa da nufin kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Isra'ila da Libya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Haaretz ta ruwaito cewa "Saddam Haftar" ya isa a cikin jirgin "Falcon" zuwa filin jirgin sama na Ben Gurion "Tel Aviv", wanda ya taso daga Dubai, a kasar UAE.

Rahoton ya ce ziyarar wadda ba a sanar da ita ba, ta dauki tsawon sa’a daya da rabi, kuma ta hada da ganawa da bangarori na tsaro na gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Jaridar ta yi hasashen cewa ziyarar dan Haftar a Isra'ila na da nasaba da zaben shugaban kasar Libya da aka shirya gudanarwa a ranar 24 ga watan Disamba mai zuwa.

A cewar Haaretz, an yi ganawar sirri tsakanin Khalifa Haftar da wasu jiga-jigan kungiyar leken asirin Isra'ila Mossad a kwanakin baya.

Mossad na gudanar da ayyuka a asirce tare da wasu kasashen larabawa wadanda ba su da shelanta kulla hulda da Isra’ila ba a bayyane.

Har yanzu dai babu wani karin haske daga bangaren haftar kan abin da jaridar yahudawa ta Haaretz ta buga.

342/