24 Oktoba 2021 - 20:32
​Jordan: Wata Cibiyar Nazari Ta Fitar Da Wani Rahoto Kan Musulmi Masu Karfin Fada A Ji

Cibiyar nazarin addinin Islama da ke Amman a kasar Jordan ta fitar da rahotonta na bana wanda a cikinsa ta saba fitar da jerin sunayen musulmi 500 mafiya karfin fada a ji a duniya.

Sabon rahoton binciken wanda shi ne na 12 da cibiyar ta fitar ya ambata cewa shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ne musulmi mafi karfin fada a aji a duniya.

Bayansa sai Sarki Salman na Saudiyya wanda ya ke a matsayi na biyu, yayin da jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatollah Ali Khamenei yake na uku a jerin musulmi masu karfin fada a ji a duniya, kamar yadda cibiyar nazarin addinin Islama da ke Amman a Jordan ta bayyana.

Sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya sun hada da yan kwallon kafa inda cibiyar ta bayyana dan kwallon Masar Mohamed Salah a matsayin na 42.

Sauran ƴan kwallon da ke cikin jerin sunayen sun haha da Sadio Mane da Paul Pogba da Zinedine Zidane.

Cibiyar ta kuma kiyasta yawan musulmi a duniya cewa ya kai biliyan 1.9, kwatamkwacin kashi 26 na yawan al'ummar duniya.

342/