Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Taron wanda ya samu halartar ministoci da tawagogi daga kasashen ketare a yayinsa kasashen duniya sun sha alwashin taimakawa hukumar zaben Libiya domin shirya zabe mai sabta.
A nasa bangare firaministan riko na Libiya, Abdel hamis Dbeibah, ya yi alkawarin cewa zaben zai gudana kamar yadda aka tsara a ranar 24 ga watan Disamba, duk da sabanin dake akwai tsakanin masu rikici a gabashin kasar.
Taron na ranar Alhamis, ya kuma tabo batun kasancewar mayakan ketare a kasar ta Libiya, inda bangarori a kasar suga gabatar da shirinsu na janye sojojin ketare daga kasar.
342/