18 Oktoba 2021 - 14:46
Rasha: Mayakan Jibhatunnusrah Sun Kai Hare-Hare A Lardin Idlin Na Arewacin Siriya

Kungiyar ‘yan ta’adda ta Jibhatunnusra da ke yankin Idlib na arewacin kasar Siriya sun kai hare-hare masu yawa a cikin lardin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Cibiyar sojojin kasar Rasha wacce take tattabar da an ci gaba da tsagaita budewa juna wuta ta Hamimim a yankin da aka ware na lardin Idlib ya bada sanarwan cewa mayakan Nusra sun kai hare-hare masu yawa a yankin.

Tashar talabijin ta Rusiyal Yaum ta nakalto cibiyar sojojin kasar ta Rasha tana cewa mayakan na Nusra sun kai hare-hare kan wurare har 45 a yankin.

Labarin ya kara da cewa wannan ya nuna cewa kungiyar ‘yan ta’addan ta sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta ta Lazikiyya, Hama da kuma Idlib da aka cimma tsakaninsu da gwamnatin kasar Syriya a baya.

Kafin haka dai sojojin kasar Syriya sun fatattaka mayakan yan ta’adda ta Nusra a wurare da dama a arewacin kasar ta Siriya, amma tare da taimakon kasar Turkiyya a halin yanzu suna rike da wasu yankuna a arewaci kasar ta Siriya wadanda suka hada da lardin Idlib. Inda a halin yanzu suke sabawa yarjejeniyar tsagaita bude wutan da suka cimma da gwamnatin kasar Siriya.

342/