14 Oktoba 2021 - 11:49
​ALGERIYA: Isra’ila Na Shirya Makarkashiya Ga Zaman Lafiyar Kasarmu

Aljeriya ta bayar da cikakkun bayanai game da makirce -makircen da Isra’ila ke shirin yi wa zaman lafiyar kasar

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A yammacin jiya Laraba, gidan talabijin na Aljeriya ya watsa wani shirin talabijin mai taken "Faduwar Hanyoyin Ruwa", wanda ya hada da ikirarin mutanen da ke cikin kungiyar 'yan aware ta "MAK" game da ayyuka da suka shafi makamai.

Binciken da hukumomin suka wallafa ya tabbatar da cewa, wadanda ke da hannu wajen hulda da bangarori na Isra’ila da sunan cibiyoyin “kungiyoyin farar hula”, suna da alaka ta kai tsaye da wannan kungiya da ke hankoron wargaza kasar Aljeriya.

Hukumomin kasar ta Algeria sun bayyana cewa, an gano makamai, kayan aikin soji, tutoci da takardu a hannun kungiyar.

Sanarwar da ofishin Babban Daraktar Tsaron Kasa ya fitar ta ce, “Mambobin wannan kungiyar ta’addanci sun kasance suna hulda da jam’iyyun kasashen waje a ko da yaushe, suna gudanar da ayyukansu karkashin inuwar kungiyoyin fararen hula da suke da mazauni a cikin Isra’ila.

Haka nan kuma sanarwar ta tabbatar da sa hannun wata kasa ta arewacin Afirka, tana mai ishara da kasar Morocco.

Wannan bayanin dai na zuwa, biyo bayan wata sanarwa ta ofishin Babban Daraktan Tsaron Kasa na Aljeriya, da ke sanar da cewa ta dakile wani yunkuri na wata kungiyar 'yan ta'adda da ke dauke da makamai a Aljeriya, wanda kuma a cewar bayanin tun a shekara ta 2014 aka fara aiwatar da wannan makarkashiya.

Jaridar Al-Anhar ta Aljeriya ta ba da rahoton cewa, ikirarin wadanda aka kama mambobin kungiyar "Mac" ya kara tabbatar cewa lamarin dama shiryayye ne.

342/