Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) -ABNA- ya kawo cewa: Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a safiyar yau Laraba ce cibiyar kare sararin samaniyar kasar Iran ta Majeed da kuma ta ‘IRGC Aerospace’ da ke Desful suka gwada garkuwan makamai masu linzami sabo, kirar cikin gida, da nufin wargaza makamai masu linzami na makiya, kuma sun gwada shi tare da samun nasarar kakkabo wani makami mai linzami da aka cillan kan daya daga cikin cibiyoyin.
A jiya Talata ce hadin guiwan sojoji da dakarun IRGC suka fara wani gagarumin atisai na wannan shekara, wanda aka sanyawa suna ‘Masu kare sararin samaniyar Waliya ta 1,400’ a lardin semnan da ke tsakiyar kasar.
Babban kwamandan dakarun kare sararin samaniyar kasar Iran na sansanin Khatamul Anbiya Burgediya Janar Qadir Rahimzadeh ya bayyana cewa manufar atisayin bana ita ce karfafa garkuwan makamai masu linzami, masu kare sararen samaniyar kasar.
Rahimzadeh ya kara da cewa kokarinsu shi ne tabbatar da ingancin garkuwan makaman sama, wadanda zasu kare cibiyoyi da wurare masu muhimmanci a cikin kasar Iran daga makaman makiya.
342/