13 Oktoba 2021 - 12:52
Mataimakin Babban Jami'in Harkokin Waje Na EU, Zai Ziyarci Iran

A wani lokaci gobe Alhamis ne ake sa ran mataimakin babban jami’in kula da harkokin kasashen kungiyar tarayyar turai, kana kuma wakilin EU a tattaunawar Vienna kan farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran zai kawo wata ziyara a Tehran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya sanar da cewa Enrique Mora zai ziyarci Tehran a gobe Alhamis.

Saeed Khatibzadeh, yayin amsa tambayoyin manema labarai ya yi nuni da ziyarar Enrique Mora zuwa Tehran, wanda shi ne mataimakin babban jami'in harkokin waje na EU Josep Borrell.

Khatibzadeh ya ce wannan ziyarar ci gaba ne na tuntubar juna tsakanin bangarorin biyu kan batutuwan da suka shafi moriyar juna, gami da alakar Iran da Tarayyar Turai, batun Afghanistan da kuma yarjejeniyar nukiliyar Iran.

342/