13 Oktoba 2021 - 12:47
Kotun Mdd Za Ta Sanar Da Hukumci A Rikicin Iyakoki Tsakanin Kasashen Sumaliya Da Kenya

Rahotannai sun bayyana cewa mai yi wu wa ne Hukucin da kotun za ta sanar ya haifar da babbar baraka ga alakar da ke tsakanin kasashen biyu game da ikirarin da kowacce kasa ta ke yi na hakkin yin amfani da Albarkatun kasa da kuma arzikin man fetur da iskar gas dake wajen, kasar Sumaliya ce ta shigar da kara a gaban kotun shekaru 7 da suka gabata

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tuni dai kasar Kenya ta zargi babbar Kotun da nuna babanci don haka ta sanar cewa ba za ta amince da hukuncin da za ta yanke ba,

Kasashen biyu suna takaddama ne kan mallakar wani wuri da ya kai fadin mita mura’bba’i 100,000 a tekun indiya da ke da dinbin arzikin danyen manfetur da iskar gas,

Kasar Kenya ta bawa wani kamfanin hakar da ma’adinai na kasar Italiya damar fara ayyukan a wajen, sai dai kasar sumaliya ta nuna rashin amincewarta da wannan matakin.

342/