Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya sanar a yau Laraba a birnin Moscow, yayin wani taron manema labarai da takwaransa na Iran Hossein Amir Abdollahian.
Lavrov ya jaddada cewa "yunƙurin da wasu ƙasashe da dama suke yi na danganta yarjejeniyar nukiliya da rangwamen da Iran ta yi kan wasu batutuwa, hakan ba shi da wata alaka.
Ya kuma kara da cewa, "mun tattauna a yau akan shirin kawance tsakanin kasashen Caucasus guda uku, wato Azerbaijan, Armenia da Jojiya, da kuma makwabtansu uku wato Iran, Turkiya da Rasha.
Lavrov ya yi kira da "a daina yin katsalandan daga waje a yankin Caspian," yana mai jaddada cewa "dole ne a hanzarta yin yarjejeniya kan matsayin tsari da ka’idojin da aka cimmawa kan wannan teku.
Dangane da Afghanistan, Lavrov ya ce, "Rasha da Iran na kira ga sabbin hukumomin Afghanistan da su yaki ta'addanci ba tare da kakkautawa ba."
A nasa bangaren, Amir Abdollahian ya nuna cewa "Tehran ta samu sakonni daga Amurka ta hannun masu shiga tsakani, kuma ta bayyana niyyarta na yin la'akari da muradun Iran cikin tsarin yarjejeniyar nukiliyar."
342/