5 Oktoba 2021 - 14:15
​Sweden: Mutumin Da Ke Yin Zanen Batunci Kan Ma’aiki (SAW) Ya Mutu

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, Lars Vilks Wani dan kasar Sweden da ya shahara wajen zane-zanen batunci ga anna Muhammadu (SAW) ya halaka a wani mummunan hadarin mota.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ‘Yan sandan Sweden sun tabbatar da cewa mutumin mai zanen zanen mai shekaru 75 a duniya tare da jami’an‘ yan sanda biyu da ke ba shi kariya sun gamu da ajalinsu ne a jiya, bayan karon da suka yi da wata babbar mota.

Mai magana da yawun ‘yan sandan ya kara da cewa:“ Wannan hatsari ya faru ne kamar kowane hatsarin hanya, kuma ana binciken a kan lamarin, kuma tun lokacin da aka tabbatar da mutuwar ‘yan sanda biyu a wannan hatsarin, an shiga gudanar da bincike na musamman a ofishin mai gabatar da kara na kasa.”

Vilks ya kasance ƙarƙashin kariyar 'yan sanda tun 2007 lokacin da ya yi zane-zanen batunci ga manzon Allah (SAW) lamarin da ya jawo fushin Musulmai a ko'ina cikin fadin duniya.

Matakin ya kuma haifar da martani na diflomasiyya daga kasashen Islama kan Sweden, sannan Firayim Ministan Sweden Fredrik Reinfeldt ya gana da jakadu daga kasashen Musulmi da dama don rage zaman dar-dar a kan wannan batu.

An sha kai wa Vilks hari, kamar yadda kuma a 2010 wani ya yi ƙoƙarin ƙona gidansa, saboda wannan dalili ko da yaushe jami'an 'yan sanda suke ba shi kariya tare da gadin gidansa.

342/