28 Satumba 2021 - 07:55
Gwamnatin Sudan Ta Cimma Matsaya Da Masu Bore

Gwammatin Sudan ta sanar da cimma matsaya tsakaninta da masu bore da suka toshe hanyoyin shiga tashar jiragen ruwa da hanyoyin shigar da man fetur a cikin kasar daga Sudan ta Kudu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Hakan dai na nufin yanzu za’a ci gaba da shigar da man fetur a kasar daga makobciyar kasar Sudan ta Kudu, bayan da masu bore suka toshe hanyoyin na tsawon kusan kwanaki goma, kamar yadda gwamnatin Khartoum ta sanar

Masu zanga zangar sun amince da tayin da tawagar ministocin da gwamnatin Khartoum ta aike domin tattaunawa da masu boren a yankin Bashayer.

Yankin dai ya kunshi babbar tashar ruwa dake kan iyaka da Sudan ta Kudu, inda ta nan ake shigo da man fetur a kasar.

A yankin wanda kusan ta nan ne ake shigar da kusan illahirin kayayakin kasuwanci a kasar, mazauna yankin na kokawa da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma da ‘ya tawaye, wacce a ganinsu bata basu damar samun cikakken wakilci a hukumomin yankunan.

342/