Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : na kasar Iran y ace UNAMA tawaga ce ta harkokin siyasa ta MDD wacce majalisar ta samar bisa bukatar gwamnatin kasar Afganistan a baya, kuma aikinta shi ne taimakawa gwamnatin kasar wajen tsare-tsare da ayyukan gudanarwa don dawo da zaman lafiya mai dorewa a kasar.
Kwamitin ya tsawaita aikin tawagar zuwa ranar 17 ga watan Maris na shekara ta 2022 mai zuwa. Sannan bayan da ta tsawaita aikin tawagar a jiya jumma’a ta kuma gwamnatin Taliban ta Afganistan ta kafa gwamnatin hadin kan kasa, wacce za ta samarda da wakilci ga dukkanin kabilun kasar, ta kuma dawo da zaman lafiya mai dorewa a kasar.Quote
Har’ila yau kwamitin tsaron ya bukace ta ta yi ya ki da ayyukan ta’addanci da kuma hana noman kwayoyi masu sa maye a kasar.
342/